Tsohon Kantoman Ƙaramar Hukumar Gwale Honarabul Abubakar Mu’azu Yusuf (Mojo), ya bayyana Gwamnatin jihar Kano a matsayin wadda tayi Kyakykyawan tanadi ga Matasa.
Abubakar Mojo ya bayyana hakan ne a yayin da yake miƙa ragamar Shugabancin ƙaramar hukumar Gwale ga Daraktan mulki na ƙaramar hukumar Alhaji Auwalu Zubairu, inda ya ce Gwamnatin tayi tanadin ne domin inganta rayuwar su duba da sune ginshiƙin kowacce al’umma.
Adan haka ya buƙaci Matasan ƙaramar hukumar Gwale dama na jihar Kano gaba-ɗaya, da su ci-gaba da bawa Gwamnatin haɗin kai da goyon baya domin ta sami damar gudanar da ayyukan da zasu bunƙasa rayuwar su dama na sauran al’ummar jihar.
A ƙarshe ya yabawa Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dama ɗaukacin Ma’aikatan da suka yi aiki da su, a bisa gudunmawar da suka bashi a tsawon watanni shidan da yayi yana jagorancin ƙaramar hukumar.
Honarabul Mojo dai ya ajiye muƙamin Kantoman ne domin ya sami damar tsayawa takarar Shugabancin ƙaramar hukumar ta Gwale, kamar yadda doka ta tanada.