Ƙungiyar Samarin Tijjaniyya ta Najeriya tayi Allah-Wadai tare da nuna rashin Jin daɗinta, bisa tashin gwauron zabin da man fetir yayi a fadin Ƙasar.
Matsayar Kungiyar tazo ne biyo bayan sanarwar da kamfanin man fetir na Kasa NNPCL yayi na ƙara farashin man a jiya Laraba
Sanarwar da Sakataren Kungiyar na Ƙasa Shehu Tasiu Ishaq da sakataren yaɗa labaranta Abubakar Balarabe Kofar Naisa suka sanyawa hannu ta ƙara da cewa, bisa la’akari da halin da ‘Yan kasa ke ciki akwai buƙatar a duba lamarin.
Wasan Dambe : Yadda Maza Suka Kwashi Kashinsu A Hannu.
Kungiyar ta bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rage farashin Man fetir ɗin, a maimakon ya ƙara shi domin sauƙaƙawa al’ummar Najeriya.
A ƙarshe sanarwar ta buƙaci al’ummar Najeriya su ci-gaba da yin addu’oin neman samun sassaucin al’amura da samun cikakken tsaro da wadatar arziƙi a Ƙasa baki-ɗaya.