Home / Labarai / Kano : Zamu Ɗauki Mataki Kan Kamfanoni Masu Zaman Kansu Tunda Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Gaza – UDHR.

Kano : Zamu Ɗauki Mataki Kan Kamfanoni Masu Zaman Kansu Tunda Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Gaza – UDHR.

Kano : Zamu Ɗauki Mataki Kan Kamfanoni Masu Zaman Kansu Tunda Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Gaza - UDHR.

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adama ta Declaration of Human Right (UDHR) dake jihar Kano, tayi alƙawarin ɗaukar matakin Shari’a akan dukkan Kamfanonin dake takewa Ma’aikata haƙƙoƙin su a faɗin jihar.

Babban Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da jaridar GTR HAUSA, inda ya ce matakin ya zama dole a sakamakon yadda ƙorafe-ƙorafen Ma’aikatan ya cika ofishin ƙungiyar tasu na yadda suke fuskantar cin zarafi dama take musu haƙƙoƙin su.

Galadanci ya ƙara da cewa ƙungiyar ƙwadago ta gaza sauke nauyin ta na nemawa Ma’aikatan haƙƙin su, adan suke Zargin an haɗa kai da su wajen gallazawa Ma’aikatan musamman ƙanana.

A cewar Babban Daraktan ” Nan bada jimawa ba zamu bayyana sunayen kamfanonin dake azabtar da Ma’aikatan su, domin duniya ta san irin abinda suke aikata wa na zalinci da rashin tausayin na ƙasa”.

Bugu da ƙari ta bayyana yadda irin matsalar take faruwa a wasu Ma’aikatun Gwamnatin jihar, na yadda wasu manyan Ma’aikata suke cinye haƙƙoƙin na ƙasa dasu saboda sun kusa kammala wa’adin aikin su.

Baya ga yadda suma ƙungiyoyin ƙwadagon dake irin waɗannan Ma’aikatu suka rufe idanuwan su, ake ta cutar da abokan aikin su ba tare da sunyi wani yunƙuri na ƙwato musu haƙƙinsu ba.

Adan haka ne ƙungiyar ta buƙaci Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ya binciki lamarin, ta yadda za’a ƙwatowa Ma’aikatan jihar haƙƙin su kuma a hukunta masu zalintar su domin ya zama izina ga ‘yan baya.

A ƙarshe ƙungiyar tayi fatan dukkan ɓangarorin da waɗannan batutuwa suka shafa zasu ɗauki dukkan matakan da suka dace, wajen tsamo Ma’aikatan kamfanonin dama na Gwamnatin jihar daga tarin ƙalubalen da suke fuskanta.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar