An zartarwa wasu ƴan asalin Najeriya guda biyu hukunci kan laifin sanadin mutuwar wani matashi ɗan ƙasar Amurka.
‘Yan uwan junan ƴan asalin Legas sun zama silar Mutuwar Matashin da suka yaudara ta hanyar lalata a intanet.
Sunja ra’ayin Jordan DeMay harya tura musu hotunansa na tsaraici, bayan sunyi ƙaryar mace ce daga baya suka ci amanarsa.
DeMay wanda yayi fice a wasan tsere ya kashe kansa ne, ƙasa da sa’a shida da fara maganarsu a Instagram.
An yankewa Matasan Samuel Ogoshi da Samson Ogoshi hukuncin ɗaurin shekara 17 da wata shida a gidan yarin Amurka.
Sun tura masa saƙon neman zama abokin Instagram bayan sunyi ƙaryar mace ce kyakkyawa inda suka ci-gaba da kalaman batsa.
Bayan samun hotunansa batsarsa sai suka nemi ya basu daloli, harma sukayi barazanar yaɗasu a internet matuƙar bai basu ba
Kuma tuni ya tura musu kuɗi iya ƙarfinsa, harya shaida musu cewa zai iya kashe kansa idan har suka yaɗa.
Mahaifiyar Jordan, Jenn Buta, tayi maraba da hukuncin, amma tace babu wani sakamakon daya dace game da shari’ar.
Wannan ne karon farko da aka hukunta ƴan Najeriya kan yaudara ta hanyar lalata a Amurka.