Home / Education / Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar Komawa Makaranta A Faɗin Jihar.

Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar Komawa Makaranta A Faɗin Jihar.

Gwamnatin Kano Ta Sanya Ranar Komawa Makaranta A Faɗin Jihar.

 

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar komawa Makaranta, domin ci-gaba da ɗaukar karatu a sabon zango na shekarar 2024/2025.

Daraktan wayar da kan Jama’a a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Inda ya ce ɗaliban dake Makarantun kwana zasu koma a gobe Lahadi 8 ga watan Satumba, su kuma ɗaliban jeka ka dawo zasu koma Jibi Litinin 9 ga watan Satumbar na shekarar 2024.

Haka kuma Makarantun da za’a koma karatun sun haɗar da Furamare, ƙaramar Sakandire da kuma babbar Sakandire.

Adan haka sanarwar ta buƙaci iyayen yara da su kiyaye ranar komawar, ta hanyar bin ƙa’idar da aka sanya domin a sami damar fara ɗaukar darasin cikin nasara.

Kwamishinan Ilimi na jihar kano Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bada tabbacin hukunta Ɗaliban da suka ƙi komawa Makarantar a lokacin da aka sanya.

Bugu da ƙari Doguwa ya shawarci Ɗaliban su guji komawa Makarantar da dukkan abubuwa da aka hana, domin bin doka da oda dama samun dama cin gajiyar ilimin da suka je koya.

Kwamishinan ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na samar da ingantaccen ilimi ga kowanne ɗalibin dake jihar, ta hanyar ɗaukar matakan da zasu samar da yanayin koyo da koyarwa me kyau a dukkan Makarantun jihar.

Harma ya bada tabbacin sanya idanu a dukkan Makarantun jihar ta hanyar yin zagayen gani da Ido, domin tabbatar da cewa komai na tafiya yadda aka tsara.

A ƙarshe Kwamishinan yayi wa Ɗaliban, Malamai dama dukkan sauran mutanen dake fannin fatan yin zangon karatun cikin nasara da kwanciyar hankali.

About gtrhausa

Check Also

Talauci Ya Sanya Ɗaliban Wata Jami'a Sata, Domin Su Ƙarasa Karatunsu

Talauci Ya Sanya Ɗaliban Wata Jami’a Sata, Domin Su Ƙarasa Karatunsu

            Daga Bashir Gasau.   Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi, …

2 comments

  1. Fatan Alkhairi, Fatan Nasara, dacewa, da Addu’oi Allah ya kara martaba. Allah ya tsare dukkan Sharri. Allah yasaka da Alkhairi. Muna godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar