Home / Labarai / Iftila’i : Cikin Awanni 5 Ambaliyar Ruwa Da Rushewar Gida Sun Sake Sanadiyyar Mutuwar Mutane Uku Da Jikkatar Wasu A Kano.

Iftila’i : Cikin Awanni 5 Ambaliyar Ruwa Da Rushewar Gida Sun Sake Sanadiyyar Mutuwar Mutane Uku Da Jikkatar Wasu A Kano.

Iftila'i : Cikin Awanni 5 Ambaliyar Ruwa Da Rushewar Gida Sun Sake Sanadiyyar Mutuwar Mutane Uku Da Jikkatar Wasu A Kano.

Lamarin ya faru ne daga ƙarfe 04:00 na yammacin jiya zuwa 8:27 na daren jiya Juma’a, a unguwannin Panisau Kwanar Ɓaure, Ɗandago kusa da Furamare, Titin Jami’ar Bayero kusa da Ofishin ‘yansandan (M T D), da kuma titin Airport.

Kakakin hukumar PFS Saminu Yusif Abdullahi ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA a yammacin yau Asabar.

kiran farko yazo ne daga unguwar Panisau Kwanar Ɓaure da misalin ƙarfe 04:00 na yamma, inda wata matashiya me suna Chimeze Diniel ta tsallake rijiya da baya.

A sakamakon ambaliyar ruwa da ta sanyata hawa rufin kwano, kafin daga bisani Jami’an hukumar suyi nasarar sauko da ita ba tare da wata matsala ba.

Sai kira na biyu daga Titin Jami’ar Bayero kusa da Ofishin ‘yansandan MTD da misalin ƙarfe 04:31 na yamma, inda aka gano gawar wani yaro a cikin ruwan dake daura da wurin kamar yadda mutanen wurin suka tabbatar, harma Jami’an hukumar suka damƙa gawar a hannun ‘yansandan Ƙwalli.

Haka kuma kira na Uku daga titin Airport da misalin ƙarfe 07:58 na dare inda shi kuma aka tsinci gawar wani Matashin me kimanin shekaru 31.

Kamar yadda likitocin Asibitin Malam Aminu Kano suka tabbatar da mutuwarsa harma suka miƙa gawar ga ‘yansandan Nomans land.

Sai kira na ƙarshe daga unguwar Ɗandago kusa da Furamare da misalin ƙarfe 08:39 na daren jiya, inda wani gini ya rushe akan wasu mutane 5 inda likitoci suka tabbatar da rasuwar ɗaya sauran huɗun kuma aka basu kulawar gaggawa.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar