Mai magana da yawun shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, Chief Ajuri Ngelale, ya ajiye aikinsa sakamakon rashin lafiya.
Ngelale ya bayyana hakan ne a wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar a yau Asabar, inda ya ce ya ɗauki wannan matakin ne bayan tuntuɓar iyalansa a yayin da rashin lafiyarsa ke ƙara tsananta a gida.
A cewar Ajuri “A ranar Juma’a, na miƙa takarda ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, inda nake shaida masa cewa na tafi hutu na sai-baba-ta-gani domin mayar da hankali kan batun rashin lafiyar dake damuna, lamarin daya zama abin damuwa ga iyalai na”.
” A yayin da nake godiya kan wannan nauyi da aka ɗora min wanda yanzu ya kai matakin yanke shawarar dakatawa da aikina, a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai kuma mai magana da yawunsa.
“Baya ga yadda na kasance Jakada na musaaman ga shugaban ƙasa a fannin sauyin yanayi, haka kuma shugaban kwamitin shirin Evergreen”.
A ƙarshe ya ce zai dawo bakin aikinsa da zarar waraka ta samu kuma lokaci ya bada dama.