Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin allurar rigakafin cututtukan dabbobi dake yaɗuwa ga shanu da sauran ƙananan dabbobi.
Sanarwar Babban Daraktan yaɗa Labaran Gwamnan Ismaila Uba Misilli ce ta bayyana hakan, inda ta ce ya ƙaddamar da shirin karo na huɗu ne a Tumfure-Bashar dake Ƙaramar HukumarA
Da yake jawabi a wajen bikin, Gwamna Inuwa ya jaddada muhimmancin rigakafin kare dabbobi daga cututtukan da za’a iya magancesu, waɗanda suke barazana ga dabbobi da sana’ar noma da kiwo.
A cewar Gwamnan “Sashin kiwo na da ɗimbin damarmakin bunƙasa tattalin arziƙi da ci-gaba, shiyasa Jihar ta rungumi shirye-shiryen bunƙasa kiwon dabbobi na ƙasa (NLTP), da kuma Shirin Zamanantar da Harkokin Kiwo (L-PRES).
Adan haka yayi ƙira ga makiyaya da manoma suyi amfani da wannar dama wajen miƙa dabbobinsu don ayi musu rigakafin, duba da yadda suka samar da duk ababen da suka dace.
A hannu guda ya zayyano wasu ayyukan da suka haɗa da gina katafariyar mayanka ta zamani a jihar, kafa kasuwar shanu ta duniya, ginawa da gyara mayanku da gandun kiwo a faɗin ƙananan hukumomin jihar.
Tun farko kwamishinan noma da kiwo Dakta Barnabas Malle, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya tare da haɗin gwiwar shirin zamanantarwa da bunƙasa kiwo (L-PRES) sun samar da isassun alluran rigakafin cututtukan da za a yi wa dabbobi kimanin miliyan 3 da dubu 600 a jihar.
A nasa ɓangaren Ko-odinetan ma’aikatar noma ta tarayya a Jihar Gombe, Dakta Ibrahim Bomoi, ya bayyana allurar rigakafin da ake yiwa dabbobi zai haɓɓaka tattalin arziƙi a fannin kiwo.
A ƙarshe Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah na jihar Modibbo Yaya, ya godewa Gwamnan tare da fatan makiyayan zasu bada haɗin kan da ya kamata.