Home / Business / Mun Shiryawa Matasa Taron Wayar Da Kai, Domin Haska Musu Damarmarki A Fannin Ƙera Ababen Hawa – NADDC.

Mun Shiryawa Matasa Taron Wayar Da Kai, Domin Haska Musu Damarmarki A Fannin Ƙera Ababen Hawa – NADDC.

Mun Shiryawa Matasa Taron Wayar Da Kai, Domin Haska Musu Damarmarki A Fannin Ƙera Ababen Hawa - NADDC.

Shugaban Hukumar Kula da Ƙere-ƙere da Samar da Ababen-hawa ta Ƙasa (NADDC), Mr. Oluwemimo Joseph, yace hukumar na daf da yin wani gangamin taron bajekolin fasaha da nufin haskawa matasa damarmaki, a ɓangaren ababen-hawa da sufuri a Nijeriya.

Mataimaki na Musamman ga Shugaban hukumar kan dabarun aiki Mr. Rosilu Emmanuel ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce zasu yi haɗin gwuiwa da Ofishin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Ci-gaban Matasa, Sanya Ido da Aiwatar da ayyuka wajen aiwatar da bajekolin.

Mr. Joseph ya ƙara da cewa taron zai nunawa matasa hanyoyin samun arziƙi a ɓangaren ababen-hawa da sufuri, ta hanyar gayyato masana da masu ruwa da tsaki a harkar ƙere-ƙeren ababen-hawa da sufuri a yayin taron.

Taron, wanda za’a gudanar a ranar 11 da 12 ga watan Satumba a ɗakin taro na Musa Yar’Adua Centre dake Abuja, zai haska damarmaki a ɓangaren sabuwar fasahar amfani da iskar gas a ababen-hawa (CNG), domin amfani dashi wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma amfanin da tsarin yake da shi a ababen-hawa.

Haka kuma ya ce a yayin taron hukumar za ta ƙaddamar da gasar zanen ƙera mota mai amfani da iskar gas, domin baiwa matasa damar bajekolin fasahar su da kuma ƙarfafa musu gwuiwa a fannin.

Ga masu sha’awar shiga gasar zasu aika da fefen bidiyo na Minti 2 zuwa 3, wanda yake ɗauke da irin fasahar su a ciki zuwa Adireshin imel na naddcouncil@gmail.com daga ranar 1 zuwa 9 ga watan Satumba.

A ƙarshe ya ce Manyan baƙin da za su halarci taron sun haɗa da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Ministan Kasuwanci da Masana’antu Honarabul (Dr.) Doris Uzoka-Anite, Me taimakawa Shugaban ƙasa kan harkokin matasa, Honarabul Titilope Gbadamosi, wanda hakan zai ƙarawa Matasan ƙaimi wajen cika burin su a fannin.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar