Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ɗage ranar komawa Makaranta, domin ci-gaba da ɗaukar karatu a sabon zango na shekarar 2024/2025.
Daraktan wayar da kan Jama’a a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Lahadin nan.
Inda ya ce Kwamishinan Ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ke wannan ƙarin haske, harma ya ce an ɗauki matakin bisa wasu dalilan na gaggawa.
Haka kuma Doguwa ya ce Ma’aikatar Ilimi ta jihar zata sanar da sabon lokacin nan ba da jimawa ba.
A cewar Doguwa ” Ina so na sanar Al’umma, Ɗalibai dama iyaye cewa an ɗage lokacin komawa Makaranta, a ranar Lahadin nan 8 ga wata da kuma Litinin 9 ga watan Satumba saboda wasu dalilai na gaggawa da suka taso”.
“Kuma dalilan zasu taimaka wajen inganta yanayin koyo da koyarwar ga yaranmu, adan haka zamu sanar daku lokacin komawa na gaba kaɗan”. Inji Doguwa.
A ƙarshe sanarwar tayi fatan al’ummar da lamarin ya shafa musamman Ɗalibai da iyaye za su yi haƙuri da abinda canjin zai haifar musu, saboda ɗage lokacin komawar.