Home / Labarai / Iftila’i : Wani Mutum Me Sana’ar Rake Ya Rasa Ransa A Sakamakon Faɗawa Kogi A Haɗejia – NSCDC.

Iftila’i : Wani Mutum Me Sana’ar Rake Ya Rasa Ransa A Sakamakon Faɗawa Kogi A Haɗejia – NSCDC.

Iftila'i : Wani Mutum Me Sana'ar Rake Ya Rasa Ransa A Sakamakon Faɗawa Kogi A Haɗejia - NSCDC.

 

 

Rundunar tsaron Al’umma ta Civil Defence reshen jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar wani Mutum me sana’ar Rake, a sakamakon faɗawa Kogi a lokacin da yake ƙoƙarin shiga domin yin wanka.

Kakakin rundunar na jihar ta Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA, inda ya ce lamarin ya faru ne a Kogin Gada (Bakin Kogi) dake ƙaramar hukumar Haɗejia.

Mutumin me suna Sulaiman Potiskum ɗan kimanin shekaru 55 a duniya, ya gamu da ajalin nasa ne a jiya da safe bayan da yaje Kogin domin yin wanka.

Kuma dai Jami’an rundunar da tallafin Direbobin yankin sun sami nasarar tsamo shi baya cikin hayyacinsa, wanda kuma kafin a kaishi Asibitin ƙwararru na Haɗejia rai yayi halin sa.

Kuma bayan likitocin sun tabbatar da mutuwar sa aka miƙa gawar ga ‘yan uwansa, domin su yi masa Jana’iza kamar yadda addinin Musulunchi ya tanada.

A ƙarshe rundunar ta shawarci al’umma da su guji zuwa wanka irin waɗannan wurare a wannan lokaci, duba da yadda ake yawan samun asarar rayukan saboda ambaliyar da wuraren taruwar ruwan suke yi.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar