Home / Labarai / SERAP Ta Buƙaci Tinubu Ya Tilasta Wa NNPCL Janye Ƙarin Kuɗin Man Fetur.

SERAP Ta Buƙaci Tinubu Ya Tilasta Wa NNPCL Janye Ƙarin Kuɗin Man Fetur.

SERAP Ta Buƙaci Tinubu Ya Tilasta Wa NNPCL Janye Ƙarin Kuɗin Man Fetur.

Ƙungiyar dake fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya (SERAP), ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da matsayinsa wajen tilasta wa kamfanin mai na ƙasar (NNPCL), ya janye ƙarin farashin man fetur cikin gaggawa duba da yadda ƙungiyar ta kira ƙarin da wanda ya saɓa wa doka.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yau Lahadi, ta ce ƙarin kuɗin man fetur ɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulki tare da dokokin ƙasar game da kare haƙƙin bil-adama.

SERAP ta kuma buƙaci shugaba Tinubu ya umarci babban lauyan gwamnatin ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su binciki zarge-zargen cin hanci da almubazzarancin da ake yi wa kamfanin NNPCL.

Cikin abubuwan da ƙungiyar ta buƙaci a bincika har da kuɗin tallafin ƙwatar kai (bailout), na dala miliyan 300 da kamfanin ya karɓa daga gwamnatin tarayya a watan Agustan da ya gabata, baya ga zargin kamfanin da rashin saka ribar mai a asusun gwamnati.

Haka kuma SERAP ta ce ya kamata a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifi a NNPCL a gaban kotu domin su fuskanci hukunci, idan har an same su da laifi tare da ƙwato dukkan abin da suka sata.

A ƙarshe ƙungiyar ta danganta taɓarɓarewar lamuran kamfanin a matsayin abin da ke haifar da ƙarin kuɗin man fetur a koda yaushe a ƙasar, a sakamakon cin hanci da rashawar da ake zargin fannin man fetur da kuma kashe kuɗin gwamnati ba bisa ƙai’da ba.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar