Buɗaɗɗiyar Wasika Zuwa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya mai girma shugaban ƙasa,
Dangane da murabus ɗin da kakakin ka Ajuri Ngelale ya yi bisa dalilin raɗin kansa a baya-bayan nan, akwai matuƙar buƙatar ka cike wannan gurbi da mutumin da yake da ƙwarewa kuma ya iya aikin.
A ra’ayina na, babu wanda ya fi dacewa da cike wancan gurbi da ya wuce Abdulaziz Abdulaziz, mai taimaka maka na musamman kan harkokin yaɗa labarai na yanzu, mutum ne mai hazaƙa da gogewa, da kuma ƙwazo.
Abdulaziz yana da ƙwarewa da gogewar da zai iya riƙe wannan muƙami domin kare muhibba da kimar wannan gwamnati ta ka.
A tarihinsa, ɗan jarida ne da ya fara aiki tun daga mai ɗauko rahoto har zuwa matakin edita, inda ya yi aiki a manyan jaridu irin su Blueprint, Premium Times, da Daily Trust, ya bar tarihi mai kyau da ya ke ci gaba da yawo a faɗin Najeriya.
Abdulaziz ya sami lambobin yabo da dama ciki har da babbar lambar yabo ta Wole Soyinka Center for Investigative Journalism Award.
Mutuncinsa, sadaukantakarsa da kimarsa abar alfahari ne da koyi duk da kasancewarsa kusa da masu mulki a cikin Aso Rock Villa, domin bashi da girman kai, kuma har yanzu yana da kyakykyawar alaƙa da abokansa da abokan mu’amalarsa a harkar yaɗa labarai.
Duk da ƙalubalen da yake ciki na kare gwamnati mai ci, musamman idan aka yi la’akari da manufofin tattalin arziki da suka jawo wa ‘yan Najeriya da dama wahala, Abdulaziz yana ci-gaba da aiki tukuru tare da jajircewa wajen fadakar da jama’a kokarin gwamnatin, harma ya na tunatar da ’yan Najeriya cewa nan gaba za’a fita daga cikin mawuyacin halin da ake ciki, baya ga yadda ya ke amfani da ƙwarewarsa a fannin yaɗa labarai wajen gudanar da aikinsa cikin hikima .
Ba iya ƙwarewar aiki kaɗai Abdulaziz yake da ita ba, a ƙashin kansa yana da kyawawan halaye na mu’amalantar kowa, Inda ya mayar da abokansa tamkar yan uwansa na jini.
Na san shi ba kawai don gwanintarsa ba har ma da halayensa na kashin kansa, domin kuwa waɗannan halaye na sa suna ƙara masa daraja a wajen mutane da dama, a ciki da wajen masana’antar yaɗa labarai.
Adan haka naɗa Abdulaziz Abdulaziz a matsayin mai magana da yawun ka zai yi kyau sosai, domin zai yi amfani da kwarewa wajen kare muhibbar gwamnatinka.
Shahararsa, musamman a yankin Arewacin ƙasar nan inda ya fito zai ƙara inganta alaƙa da gwamnatin ku da yankuna daban-daban.
A matsayina na ɗan Najeriya kuma mai sharhi kan al’umma, ina rokonka, mai girma shugaban ƙasa, da dukkan masu girma makusantan shugaban ƙasa, ku bawa wannan shawara tawa kulawa ta musamman domin kuwa Abdulaziz Abdulaziz ne ya fi cancanta da wannan muƙami.
Na bada wannan shawarar ne ba’a matsayin aboki ba kawai, saboda yaƙinin cewa Abdulaziz Abdulaziz shi ne mutumin da ya fi cancanta ya gaji Ajuri Ngelale a matsayin kakakin shugaban kasa .
Na gode,
Nasiru Zango
7 ga Satumba, 2024.