Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an kama Ajaero ne da safiyar yau Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Ajaero na kan hanyar sa ta zuwa ƙasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance.
An bukaci shugaban NLC ya halarci taron Ƙungiyoyin Ƙwadago da za a yi a Landan, wanda za’a fara yau.