Home / Labarai / SERAP Tace Jami’an DSS Sun Yiwa Ofishinta Ƙawanya.

SERAP Tace Jami’an DSS Sun Yiwa Ofishinta Ƙawanya.

SERAP Tace Jami'an DSS Sun Yiwa Ofishinta Ƙawanya.

 

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) sun kai sumame ofishin ƙungiyar SERAP, mai fafutikar yaƙi da cin hanci da Rashawa a Abuja.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa jami’an tsaron sun yi wa ofishinsu ƙawanya ne ba bisa ƙa’ida ba, tare da neman ganawa da manyan daraktocin ƙungiyar.

Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasar, Bola Tinubu da ya shiga tsakani, sannan ya umarci jami’an su daina abin da ƙungiyar ta kira ”tsangwama da cin zarafi, da kuma take haƙƙin ‘yan Najeriya”.

Kawo yanzu dai babu cikakken dalilin da yasa jami’an tsaron suka mamaye ofishin SERAP ɗin.

Hakan na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar NLC, ta sanar da cewa jami’an na DSS sun kama shugabanta, Joe Ajero a filin jirgin saman Abuja.

 

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar