Home / Education / Wajibi Gwamnatin Tarayya Dana Jihohi Su Haɗa Kai, Wajen Fito Da Manufofin Da Talaka Zai Sami Sauƙin Rayuwa.

Wajibi Gwamnatin Tarayya Dana Jihohi Su Haɗa Kai, Wajen Fito Da Manufofin Da Talaka Zai Sami Sauƙin Rayuwa.

Wajibi Gwamnatin Tarayya Dana Jihohi Su Haɗa Kai, Wajen Fito Da Manufofin Da Talaka Zai Sami Sauƙin Rayuwa.

 

Gogaggen Ɗan Jaridar nan a Najeriya Alhaji Muhammad Sulaiman Gama ya shawarci gwamnatin tarayya da Jihohi, akan su haɗa kai wajen fito da manufofin da zasu magance wa Talakawan ƙasar matsalolin da ke damun su.

Gama na bada shawarar ne ta cikin wata buɗaɗɗiyar Wasiƙa da ya fitar kuma ya aiko wa jaridar GTR HAUSA a safiyar yau Litinin, inda ya ce akwai auren rashin fahimta tsakanin Gwamnatin Tarayyar da kuma na Jihohi.

Kuma dai bayanin nasa yazo ne biyo bayan jawabin da Shugaban ƙasa Tinubu yayi wa ‘Yan Najeriya mazauna ƙasar China, inda yake bayyana tsare-tsaren da Gwamnatin sa ke yi na ƙawata ƙasar ba tare da nema wa Talaka mafitar ƙuncin da yake ciki ba.

A cewar gogaggen Ɗan Jaridar “Gwamnatin Tarayyar ta maida hankali wajen samar da hanyoyi dama sauran ayyukan ƙawata ƙasa, kamar aikin titin da zai laƙume Naira Tiriliyan 15”.

A inda su kuma Gwamnatin Jihohin ƙasar suka maida hankali wajen yin ayyukan kwangila kamar gadoji da sauran gine-ginen da zasu sami riba idan sunyi.

Wanda kuma dukkan ayyukan suna faruwa ne a dai-dai lokacin da talakawan ƙasar suke cikin matsananciyara yunwa da ƙangin rayuwa.

Adan haka Gama wanda shine shugaban kamfanin Shafga GLobal Concept Nig Ltd, ya ce ya zamar wa Shugabannin ƙasar wajibi su karkato da hankulan su, wajen haɗuwa a manufa guda wadda zata dawo da talaka cikin hayyacinsa.

Harma ya ce yiwa al’umma ayyukan da suka fi buƙata shine ya bambanta mulkin dimokraɗiyya dana Soja.

Tunda shine ake amfani da ƙarfin Bindinga wajen aiwatar da abubuwa koda talakawa basa so, amma sai gashi ana gwada hakan a wannan Gwamnatin.

Bugu da ƙari ya shawarci dukkan masu riƙe da madafun iko su jingine dukkan wasu ayyuka, domin magance wa Talakawan ƙasar matsalar yunwar da ta addabe su, inganta fannin lafiya, Ilimi da kuma Noma da Kiwo.

A ƙarshe yayi fatan mahukuntan ƙasar a matakai daban-daban zasu yi amfani da dukkan shawarwarin daya basu, domin ya zama sun sauke nauyin da yake wuyan su kuma sun inganta rayuwar talakawan ƙasar.

 

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar