Home / Labarai / Sarkin Kano Yayi Alƙawarin Taimakawa Kwamitin Unguwar Ɗorayi Domin Magance Matsalar Tsaro.

Sarkin Kano Yayi Alƙawarin Taimakawa Kwamitin Unguwar Ɗorayi Domin Magance Matsalar Tsaro.

Sarkin Kano Yayi Alƙawarin Taimakawa Kwamitin Unguwar Ɗorayi Domin Magance Matsalar Tsaro.

 

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammdu Sanusi na biyu, yayi alƙawarin taimakawa kwamitin tabbatar da tsaron unguwar Ɗorayi da kewaye domin magance matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Sarkin na wannan jawabi ne a yayin da ya karɓi baƙuncin kwamitin yankin a fadarsa, inda ya ce Masarautar za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an magance matsalar tsaron.

Haka kuma Sarki Sanusi ya ƙara da cewa, yana matuƙar tausayawa al’ummar yankunan da matsalar take damu, duba da irin illolin da hakan ke haifarwa.

Malam Abdullahi Idris Ɗan fodiyo yana cikin iyayen kwamitin tsaron na unguwar ta Dorayi da kewaye, ya yi wa Sarkin cikakken ƙarin haske akan matsalar tsaron da ta addabi yankin wadda take neman sabauta rayuwar su.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan da fitowa daga masarautar, Ɗan Fodiyo ya bayyana ƙoƙarin da masana’antun Kano suke yi musu wajen magance matsalar tsaron yankin.

A ƙarshe dukkan ɓangarorin biyu sun yi fatan samun zaman lafiya a jihar Kano dama ƙasa baki-ɗaya.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar