Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya sake naɗa Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe a karo na biyu, a matsayin Shugaban Asibitin bayan ƙarewar wa’adin sa na Farko.
Cincirondon Ma’aikatan dai sun bayyana farin cikinsu matuka, a bisa bawa shugaban nasu damar sake Jagorantar Asibitin, duba da irin managartan tsare-tsaren da ya kawo a wa’adin mulkin sa na farko.
A nasa jawabin shugaban Asibitin (CMD) Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, ya bayyana godiyarsa da Shugaba Tinubu a bisa wannan dama da ya sake bashi, inda yayi alƙawarin ciyar da Asibitin gaba.
Haka kuma ya yaba wa Ma’aikatan a bisa yadda suke jajircewa akan aikin su na hidimtawa al’umma, harma ya hore su da su ƙara zage damtse wajen sauke nauyin da ke wuyansu.
A ranar 5 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ne Shugaba Tinubu ya sake naɗa Farfesa Sheshe a matsayin Shugaban Asibitin Malam Aminu Kano, inda zai sake shafe shekaru 4 a wannan wa’adin da ya kasance na biyu kuma na ƙarshe.