Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja.
Hafsan Hafsoshin Najeriya Janaral Christopher Gwabin Musa, ya jajantawa waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin Jihar Borno.
Daraktan yaɗa labaran Ma’aikatar tsaron Najeriya Birgediya Janar Tukur Gusau ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce suna miƙa saƙon jaje ga Gwamnatin jihar Borno dama dukkan al’ummar da lamarin ya shafa.
Haka kuma ya bayyana Iftila’in a matsayin abin taɓa zuciya, duba da yadda ya yi Sanadiyyar rasa rayukan al’umma, dukiyar da ba’a san adadinta ba, dama raba dubban al’umma da muhallansu.
Haka kuma Janaral Musa ya bada tabbacin cewa, rundunar zata yi haɗin gwuiwa da hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), dama dukkan sauran Hukumomin da lamarin ya shafa domin bawa waɗanda Iftila’in ya shafa kulawa da ta domin rage musu raɗaɗin Jarrabawar da ta same su.
Adan haka sanarwar ta miƙa saƙon jajen a madadin dukkan Ma’aikatan rundunar tsaron Najeriya, tare da fatan Allah ya jiƙan waɗanda suka Mutu, kum ya mayarwa dukkan waɗanda suka yi asarar dukiyar su da mafi alkhairi.