Hukumar dake yaƙi da sha da fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa reshen jihar Kano (NDLEA), ta ce akwai kuskure a Sanarwar da wasu kafafen yaɗa labarai suka yaɗawa.
Wadda ke cewa hukumar ta bayyana adadin ‘yan takarkarun Kujerar Shugabancin ƙaramar hukumar da ta gano suna ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi.
Kakakin hukumar na Jihar Kano Sadiq Muhammad Maigatari ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA, inda ya ce akwai kuskure a wancan labari domin kuwa babu inda suka ce sun gano ‘yan takarkarun Shugabancin ƙaramar hukumar 20 suna ta’ammali da kayan maye.
A cewar Maigatari ” Abinda hukumar mu ta faɗa shine wannan gwaji ana nan ana yinsa ba’a kammala ba, wanda kuma ya zuwa yau mun tantance ‘yan takarkaru sama da ɗari uku a matakai daban-daban”.
Toh sai dai kuma bamu da masaniyar adadin waɗanda suka fito takarar Shugabancin ƙananan Hukumomin da kuma ta Kansila, haka kuma bamu san daga waɗanne Jam’iyyu suka zo ba, duba da yadda kowa a raɗin kansa yake zuwa ba wai sunayen su aka turo mana ba.
Adan haka hukumar ta buƙaci al’umma da su ci-gaba da bibiyar ta, har zuwa lokacin da zata fitar da sakamakon binciken ta ƙarshe da zarar ta kammala.