Home / Education / Rabuwa Da Kyawawan Ɗabi’un Malam Bahaushe Ne Ya Jefa Shi Halinda Yake Ciki – Dagachin Mariri.

Rabuwa Da Kyawawan Ɗabi’un Malam Bahaushe Ne Ya Jefa Shi Halinda Yake Ciki – Dagachin Mariri.

Rabuwa Da Kyawawan Ɗabi'un Malam Bahaushe Ne Ya Jefa Shi Halinda Yake Ciki - Dagachin Mariri.

 

 

Dagacin garin Mariri dake a ƙaramar hukumar kumbotso Alhaji Saminu Garba Madaki, ya bayyana yadda matsaloli suka yiwa Malam Bahaushe katutu saboda rabuwa da Kyawawan Ɗabi’unsa da kuma al’adun sa.

Alhaji Saminu Madaki na bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa dake Mariri, inda ya yi bitar wasu daga cikin Kyawawan ɗabi’un kamar taimakon juna, girmama juna, ƙaunar juna, zumunci, neman Ilimi da sauransu.

A cewar Dagachin ” Girmama kyawawan al’adu da ɗabi’un malam bahaushe masu nagarta, zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kuma fattakar yunwa a faɗin jihar Kano dama ƙasa baki-ɗaya”.

Da yake tsokaci akan tarbiya da ingata rayuwar matasa, Madaki yace rabuwa da matasan babu sana’a ko kuma neman Ilimi na cikin dalilan dake kawo yawaitar faɗan daba da ƙwacen Waya a faɗin jihar Kano da sauran sassan ƙasar.

Adan haka ya buƙaci al’ummar Malam Bahaushe su dawo da al’adun su da ɗabi’unsu na baya, ta yadda zai zama rayuwar su ta dawo kan tsari me kyau kuma abar alfahari a kowanne yanki.

Daga ƙarshe ya shawarci mahukunta da masu hannu da shuni su dafa wa marasa ƙarfin dake zagaye dasu a cikin unguwanni dama na yankin su Gaba-ɗaya.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar