Daga Bashir Gasau.
Babban Mashawacin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Honarabul Mansur Ibrahim Maiganji, ya ce babu Shakka Maliya ya sanya farin ciki a zukatan al’ummar Kano.
Maiganji na wannan bayani ne a sakamakon yadda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau Jibrin (Maliya), ya jagoranci bada tallafin Shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta aiko da ita zuwa jihar Kano.
Kuma dai yana wannan jawabi ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido, wajen bada tallafin domin ganin yadda aikin rabon yake kasancewa.
Ya kuma ƙara da cewa, Saƙon Shinkafar Gwamnatin Tarayyar yazo a dai-dai lokacin da ake buƙatar sa, duba da yadda al’ummar suke kokawar neman abinda zasu sanya a cikin su.
Bugu da ƙari ya ce Sanatan zai ci-gaba da irin wannan abin alkhairi, domin samawa al’umma sauƙi a jihar Kano dama ƙasa baki-ɗaya.
Adan haka ne mah al’umma suke yaba masa duba da irin wannan aikin nasa na tallafawa al’umma, wanda yake karaɗe mazaɓar sa, Kano ta Arewa dama kafatanin faɗin jihar.
A ƙarshe waɗanda suka amfana da tallafin sun bayyana godiyarsu ga Sanatan a bisa yadda ya tafiyar da shirin cikin adalci, domin gujewa masu karkatar da shi ko kuma masu sanya son rai a cikin irin wannan tsari idan yazo.