Home / Labarai / Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Tsawaita Wa’adin Ma’aikata 4,000 Da Ganduje Yayi.

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Tsawaita Wa’adin Ma’aikata 4,000 Da Ganduje Yayi.

      Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Tsawaita Wa'adin Ma'aikata 4,000 Da Ganduje Yayi.         Daga Bello Usman, Kano.

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala bincike da tantance ma’aikatan da aka yi wa ƙarin wa’adin aiki bayan sun kai shekara 35 suna aiki, ko kuma sun kai shekara 60 a duniya.

Shugaban Ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa ya sanar da hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce bayan an soke ƙudurin ne, aka kafa kwamiti domin ƙididdige adadin ma’aikatan.

Aƙalla ma’aikan jihar Kano 4,000 da gwamnatin tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ta tsawaita wa wa’adin aiki ne ake sa ran zasu yi ritaya a ranar 1 ga Disamban 2024.

Ganduje ne ya assasa shirin tsawaita wa’adin aiki a jihar, inda ma’aikata za su iya ci-gaba da aiki har na tsawon shekara biyar bayan sun kai lokacin ritaya.

Toh sai dai bayan gwamna Abba Yusuf ya ɗare karagar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023 ne ya soke wannan ƙudurin, sannan ya yi umarnin a dawo da shekarun ritayar shekara 35 ana aiki ko kuma shekara 60 a rayuwa.

A cewar Abdullahi “Bayan bincike ne kwamitinmu ya gano cewa kusan ma’aikata 4,000 suke cikin wannan tsarin, amma za su yi ritaya a 1 ga Disamban 2024, Wannan na nufin a ƙarshen watan Satumba za su miƙa takardar ajiye aiki,” kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A ƙarshe ya ce gwamnati a shirye take wajen maye gurbin da za su bari bayan sun yi ritayar.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar