Daga Bashir Gasau.
Gwamnatin Kano ta sanar da sabuwar ranar komawa Makaranta, domin ci-gaba da ɗaukar karatu a sabon zango na shekarar 2024/2025.
Daraktan wayar da kan Jama’a a Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Alhamis.
Inda ya ce ɗaliban dake Makarantun kwana zasu koma a ranar Lahadi 15 ga watan Satumba, su kuma ɗaliban jeka ka dawo zasu koma ranar Litinin 16 ga watan Satumbar na shekarar 2024.
Makarantun da za’a koma karatun sun haɗar da Furamare, ƙaramar Sakandire da kuma babbar Sakandire, mallakar Gwamnati da kuma masu zaman kansu.
Toh sai dai kuma sanarwar bata bayyana dalilin da ya sanya Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna ya ɗage ainihin ranar komawa Makarantar wato 7 ga watan nan da muke ciki ba.
Adan haka sanarwar ta buƙaci iyayen yara da su kiyaye ranar komawar, ta hanyar bin ƙa’idar da aka sanya, kamar yadda Arewa Radio ta rawaito.
Bugu da ƙari an kuma shawarci Ɗaliban su guji komawa Makarantar da dukkan abubuwa da aka hana, domin bin doka da oda dama samun dama cin gajiyar ilimin da suka je koya.
A ƙarshe Gwamnatin ta sha alwashin sanya idanu a dukkan Makarantun jihar ta hanyar yin zagayen gani da Ido, domin tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda aka tsara.