Daga Bello Usman.
Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta bawa ɓangaren rage wa talakawan ƙasar raɗaɗi muhimmanci.
Wakilin IMF a Najeriya, Dokta Christian Ebeke ne buƙaci hakan a yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Arise a jiya, a dai-dai lokacin da ake ci-gaba da muhawara a kan ƙarin farashin man fetir a ƙasar.
Toh sai dai kuma ya ce har yanzu ba’a kai farashin man fetir ɗin asalin farashinsa na kasuwa ba, wanda hakan ke nuna cewa za’a ƙara farashin a nan gaba kamar yadda jaridar Vanguard ta kalato.
Idan ba’a manta ba, shi ma kamfanin NNPCL na Najeriya ya bayyana irin wannan matsayar a baya.
Babban jami’in na IMF ya bayyana damuwarsa a kan irin wahalar da ƴan Najeriya suke ciki, a sanadiyar wasu matakai da gwamnatin ƙasar ta ɗauka.
A cewar Ebeke, “Ina tunanin ƙarin farashin man ya zo ne a dai-dai lokacin da ƴan Najeriya suke cikin tsananin rayuwa.
“Domin Ƴan ƙasar suna fama da matsaloli da dama, kamar hauhawar farashin kayayyaki kamar abinci ga ambaliya da sauransu”.
A ƙarshe ya ce ƙara farashin man ya zo a dai-dai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tangal-tangal, kuma ƴan Najeriya na cikin tsananin rayuwa.