Daga Bashir Gasau.
Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta bayyana aniyar ta, na shiga zaɓen Ƙananan Hukumomin jihar dake tafe.
Sakataren yaɗa labaran Jam’iyyar na jihar Kano Honarabul Ahmad S. Aruwa ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, inda ya ce zasu shiga takarkarun Kujerun Shugabannin ƙananan Hukumomin da kuma na Kansilolin dake faɗin jihar.
Haka kuma Jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Shugaban ta Kano Honarabul Abdullahi Abbas, ta ce zata fara siyar da fom ɗin takarar daga yau Alhamis 12 ga watan Satumba zuwa ranar Asabar 14 ga watan na shekarar 2024.
Za dai a siyar da fom ɗin takarar ne a Ofisoshin Jam’iyyar na ƙananan Hukumomin Jihar, daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 5 na yammacin ranakun da aka bayyana.