Home / Flooding / Ambaliya : Muna Kira Ga Dukkan Al’ummar Sassan Duniya Su Tallafawa Al’ummar Maiduguri – UDHR

Ambaliya : Muna Kira Ga Dukkan Al’ummar Sassan Duniya Su Tallafawa Al’ummar Maiduguri – UDHR

Ambaliya : Muna Kira Ga Dukkan Al'ummar Sassan Duniya Su Tallafawa Al'ummar Maiduguri - UDHR         Daga Bashir Gasau.

 

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adama ta Declaration of Human Right (UDHR) dake jihar Kano, tayi kira ga dukkan al’ummar sassan duniya da su tallafawa mutanen Maidugurin Jihar Borno, a bisa Iftila’in da ya same su na ambaliyar ruwa.

Babban Daraktan ƙungiyar Kwamared Umar Sani Galadanci ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA, inda ya ce hakan shine abinda suke buƙata duba da babbar Jarrabawar da ta same su.

A cewar Babban Daraktan ” Muna kira ga dukkan wani wanda zai iya tallafawa al’ummar Maiduguri da kowanne irin abin buƙata ne, da ya gaggauta taimaka musu a wannan lokaci da suke tsananin buƙatar taimakon ”.

Haka kuma ƙungiyar ta Jajantawa Gwamnatin jihar dama dukkan al’ummar da Iftila’in shafa, tare da fatan Allah ya mayar musu da mafificin alkhairi.

Bugu da ƙari sanarwar ta yaba wa Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, a bisa yadda yake ta ƙoƙarin ganin ya sama wa mutanen mafita.

Adan haka ƙungiyar tayi fatan dukkan ɓangarorin da kiran ya shafa zasu taimaka wa mutanen Maidugurin, domin rage musu raɗaɗin Jarrabawar da ta same su, ta hanyar tsamo su daga halin da suke ciki.

A ƙarshe ƙungiyar ta miƙa saƙon jaje ga dukkan waɗanda Iftila’in ambaliyar ruwa, dama rushewar gidaje ya shafa a faɗin Najeriya dama duniya Gaba-ɗaya.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar