Daga Bello Usman.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 16 ga watan Satumbar da muke ciki a matsayin ranar hutun Maulidi.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin tarayya, inda ya ce an bada hutun ne don karrama bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
Sanarwar ta kuma taya al’ummar musulmi, na gida Najeriya dana ƙasashen ƙetare murnar wannan biki mai alfarma.
A ƙarshe Ministan ya buƙaci al’ummar musulmi da su yi amfani da lokacin wajen yaɗa halayen nagarta, tsakanin abokan zaman su domin samun wanzuwar zaman lafiya a ƙasa baki-ɗaya.