Home / Health / Iftila’i : Iska Me Ƙarfi Tayi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 Tareda Jikkata 15 A Kano.

Iftila’i : Iska Me Ƙarfi Tayi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 Tareda Jikkata 15 A Kano.

Iftila'i : Iska Me Ƙarfi Tayi Mutuwar Mutum 5 Tareda Jikkata 15 A Kano.                    Daga Bello Usman.

 

A makon da ya gabata ne Iska mai ƙarfin gaske ta yi sanadiyar mutuwar wasu mutane biyar, tare da jikkata wasu Goma Sha biyar a yankin ƙaramar hukumar Wudil dake jihar Kano.

Jami’in yaɗa labaran Shiyyar ta Wudil Nasiru Habu Faragai ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR HAUSA a safiyar yau Jumu’a, inda ya ce lamarin ya faru ne a sakamakon rushewar da Gidaje suka yi akan su.

Faragai ya kuma ce yanzu haka mutanen da suka jikkata suna babban asibitin kwanciya na Wudil inda suke karɓar kulawar gaggawa.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, aƙalla Magidanta sama da tamanin ne suka rasa gidajen su a sakamakon ƙaƙƙarfar Iskar.

Da yake jawabi a lokacin da ya kai ziyarar Ta’aziyya da kuma Jaje ga waɗanda Iftila’in ya shafa, Kantoman Ƙaramar hukumar Alhaji Ahmed Iliyasu Wudil ya bayyana alhininsa bisa ga faruwar lamarin.

Inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma bawa waɗanda suka jikkata lafiya, kana ya maida wa waɗanda suka rasa gidajen su da mafificin alkhairi.

A ƙarshe ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta kawo agaji, ga dukkan waɗanda suka rasa gidajen su da sauran dukiyoyin su a sanadiyar wannan iftila’i.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar