Daga Bello Usman.
Hukumar zaɓe me zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), ta rage Kuɗin fom ɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan Hukumomin Jihar dake tafe.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan, a yayin taron masu ruwa da tsaki dangane da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za’a yi a wata me kamawa.
Ya ce rage Kuɗin ya biyo bayan umarnin da kotu ta bayar, dangane da yawan Kuɗin Fom ɗin da wasu jam’iyyun adawa suka ƙalubalanta a gaban ta.
A cewar Malumfashi, ” Yanzu hukumar zaɓen ta mayar da Kuɗin Fom ɗin takarar a matakin Shugaban ƙaramar hukuma da mataimakinsa naira miliyan 9 maimakon naira miliyan 10, yayin da kuma takardar tsayawa takarar kansila aka maida shi naira miliyan 4 maimakon naira miliyan 5 da yake a baya”.
Adan haka ne ya ce shirye-shiryen hukumar ya kammala na fara siyar da Fom ɗin daga ranar Litinin mai zuwa wato 15 ga watan Satumbar nan da muke ciki.
A ƙarshe hukumar ta yaba wa jam’iyyun siyasa bisa yadda suke bai wa hukumar haɗin-kai musamman babbar jam’iyyar adawa a nan Kano ta APC, bisa amincewa da shiga zaɓen na ƙananan hukumomin jihar, wanda zai gudana a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba mai zuwa.