Home / Security / Mun kashe Halilu Sububu Saura Bello Turji Da Sauran ‘Yan Ta’adda – Janar Musa.

Mun kashe Halilu Sububu Saura Bello Turji Da Sauran ‘Yan Ta’adda – Janar Musa.

Mun kashe Halilu Sububu Saura Bello Turji Da Sauran 'Yan Ta'adda - Janar Musa.       Daga Bashir Gasau.

 

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce kwanakin ɗan bindiga, Bello Turji da sauran manyan ƴanbindiga da suka addabi ƙasar sun kusa ƙarewa, a daidai lokacin da sojoji suke ci-gaba da aiki a jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Ya ce kashe Kachalla Halilu Sububu, wanda ƙasurgumin ɗan bindiga ne na cikin nasarorin da sojojin suke samu.

Janar Christopher ya ƙara da cewa wani aikin soji na musamman mai suna “Fansar Yamma a Arewa maso Yamma,” da za a ƙaddamar ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Ya ce za a ƙara tura wasu jiragen yaƙi zuwa jihar domin ci-gaba da aikin sojin, kamar yadda babban hafsan ya bayyana a ziyararsa ga Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.

 

BBC Hausa.

About gtrhausa

Check Also

Inganta Sashen Kula Da Satar Ma'adanai Na NSCDC Yafi Ƙirƙiro Sabuwar Hukuma - Gana Muhammad

Inganta Sashen Kula Da Satar Ma’adanai Na NSCDC Yafi Ƙirƙiro Sabuwar Hukuma – Gana Muhammad

Daga Muhammad Yusif Dambo, Abuja. Tsohon Shugaban Hukumar tsaron Al’umma ta Civil Defence, Abdullahi Gana …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar