Home / Labarai / Rundunar ‘Yansandan Kano Tayi Holin Masu Ƙwacen Waya Dama Sauran Masu Aikata Laifi.

Rundunar ‘Yansandan Kano Tayi Holin Masu Ƙwacen Waya Dama Sauran Masu Aikata Laifi.

Rundunar 'Yansandan Kano Tayi Holin Masu Ƙwacen Waya Dama Sauran Masu Aikata Laifi.                      Daga Bashir Gasau.

 

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Salman Dogo Garba, ta yi holin masu aikata laifuka daban-daban.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, inda ya ce sunyi sumamen ne cikin kwanaki 12 na wannan wata na Satumba.

Rundunar 'Yansandan Kano Tayi Holin Masu Ƙwacen Waya Dama Sauran Masu Aikata Laifi.

Mutanen da suka kama sun haɗar da waɗanda ake zargi da aikata faɗan daba, ƙwacen Waya da kuma fashi da makami.

Haka kuma rundunar ta sami nasarar kama mutane 25 da kuma wayoyi 126, waɗanda da aka yi fashin su da kuma na sata.

Baya ga haka sun kuma sami nasarar kama kayan maye kala-kala, samfurin Allurar potwine (21), diazepam (20), Ƙwayar xol (600), baya ga yadda wasu mutum Uku suka gudu suka bar tabar Wiwi me ɗumbin yawa.

Rundunar 'Yansandan Kano Tayi Holin Masu Ƙwacen Waya Dama Sauran Masu Aikata Laifi.

 

Bugu da ƙari kayan da aka ƙwato a gurin mutanen da ake zargi sun haɗar da Adduna (2), Almakashi (2), Takobi (1) da kuma Na’ura me Ƙwaƙwalwa ƙirar tafi da gidanka wato Computer Laptops (2).

A ƙarshe sanarwar ta bada tabbacin gurfanar da su a gaban kuliya, da zarar ta kammala bincike domin su fuskanci hukunci dai-dai da abinda suka aikata, a inda za’a mayarwa da masu kayan da aka ƙwato kayansu bayan an tantance su.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar