Daga Bashir Gasau.
Rundunar ‘Yansandan Jihar Borno ƙarkashin jagorancin Kwamishina CP. ML Yusufu, ta girke Jami’anta a bakin gadar da ta karye domin hana Zirga-zirga a yankin.
Kakakin rundunar na jihar Borno SP Ahmed Mohammed Wakil ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aiko wa jaridar GTR Hausa a yau Asabar.
Inda ya ce matakin ya biyo bayan umarnin da Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar na hana Zirga-zirga a bakin Gadar.
Da yake ziyara aiki a wajen wannan Gada, CP Yusufu ya ce matakin ya biyo bayan shawarar da ƙwararru suka bayar.
Akan irin haɗarin da ke tattare da ragowar Gadar, wadda ta karye akan titin Lagos dake birnin Maiduguri a sakamakon ambaliyar ruwa.
Ya kuma hori Jami’an da aka girke su nuna ƙwarewa, a yayin gudanar da aikin domin kiyaye haƙƙoƙin ‘yan ƙasa.
A ƙarshe sanarwar ta Jajantawa Waɗanda Iftila’in ya shafa, tare da fatan zasu basu haɗin kai da goyon baya a wannan lokaci.