Daga Muhammad Yusif Dambo Abuja.
Ministan Albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na Najeriya, Joseph Utsev ya yi gargaɗin sake samun mummunar ambaliya a kogunan Neja da Benue.
Yayin da yake jawabi ga taron menama labarai a Abuja, babban birnin ƙasar, Ministan ya ce an samu ƙaruwar ruwan da ke ƙwarara a kogunan biyu zuwa yankin Naija Delta da ke kudancin ƙasar.
‘A yayin da muke jajanta wa al’ummomin jihohin Borno da Yobe da Jigawa da Bauchi da sauran jihohin da suka fuskanci ambaliya, muna ƙara jan hankalin ‘yan ƙasar game da yiwuwar sake fuskantar wata ambaliyar daga kogunan Benue da Neja da wasu yankunan yankin”, in ji ministan.
Kan haka ne mista Utsev ya yi kira ga mazauna yankin su ɗauki matakai domin kauce wa bala’in ambaliya a wasu sassan kudancin ƙasar.
Gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar birnin Maiduguri ke fuskantar mummunar ambaliya da ta auka wa birnin sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin.
Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya ce lamarin ya shafi kusan mutum miliyan biyu.