Daga Bello Usman.
Wani mummunar hatsarin kwale-kwale yayi sanadin nutsewar fiye da mutum 40 a garin Gummi na jihar Zamfara.
Shaidu sun tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Asabar, a mashayar ‘yan daga da ke gulbin Gummi.
Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Abubakar Umar ya ce har ya zuwa yanzu ana ci-gaba da aikin ceto mutanen da suka nutse.
A cewar Abubakar ”Kawo yanzu sarkin ruwan yankin da sauran masu iyo na ci-gaba da aikin ceto, don lalubo mutanen da kwale-kwalen ya kife da su, kuma kawo yanzu ko mutum guda ba’a kai ga cetowa ba”, kamar yadda ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa galibi waɗanda ke cikin jirgin manoma ne da ke ƙoƙarin tsallaka kogin domin zuwa gonakinsu.
Kwamishinan yaɗa labarai da bunƙasa al’adun jihar, Mannir Haidara Kaura ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sai dai ya ce kawo yanzu a hukumance ba’a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba.
Ya kuma ƙara da cewa an ceto wasu daga cikin mutanen da lamarin ya rutsa da su, kuma ana ci-gaba da aikin ceto domin zaƙulo mutanen da suka nutse cikin ruwan
Hatsarin na zuwa ne makonni bayan mummunar ambaliya ruwa da ta faru a garin na Gummi, inda ta haddasa asarar dukiya mai ɗimbin yawa.
Batun kifewar kwale-kwale dai ba sabon abu bane a Najeriya, inda a lokuta da dama hatsarin ke zuwa da muni sakamakon irin ƙazamin lodin da ake yi wa jiragen ruwan.