Daga Bashir Gasau.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce NNPC kaɗai Matatar Man Ɗangote za ta dinga siyarwa da man Fetur.
Ministan Kuɗin Najeriya Wale Edun ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar jiya a Abuja, inda ya ce NNPC zai fara karɓar Man Ɗangoten daga gobe Lahadi.
Ministan wanda Shugaban Hukumar tattara haraji ta Najeriya (FIRS), Zacch Adedeji ya wakilta ya ƙara da cewa, kashin farko na yarjejeniyar lodin man fetir ta kammala.
A cewar Edun “Daga Watan Oktoba me kamawa Kamfanin Mai na ƙasa NNPC, zai dinga bawa Matatar Man Ɗangote ɗanyen Mai ganga 385,000 a kowacce rana”.
Haka kuma Matatar Man Ɗangoten zata dinga siyar da Fetir ɗin nata ga kamfanin Man na NNPC kaɗai, a inda su kuma ‘yan Kasuwa zasu dinga Siya daga Kamfanin na NNPC.
A ƙarshe Ministan ya ce Matatar Man Ɗangote zata siyar da Man Diesel, ga dukkan masu buƙata ba tare da sa hannun NNPC ba.