Home / Labarai / Al’ummar Jihar Bauchi Sun Gudanar Da Gagarumin Maulidi

Al’ummar Jihar Bauchi Sun Gudanar Da Gagarumin Maulidi

Al'ummar Jihar Bauchi Sun Gudanar Da Gagarumin Maulidi     Daga Aliyu Gerengi Gombe.

 

Dubun dubatar al’ummar jihar Bauchi dana sassan Najeriya ne suka yi cikar kwari, a filin wasa na Abubakar Tafawa Ɓalewa domin yin gangamin Maulidin wannan shekara.

Maulidin ya gudana ne bisa jagorancin Sheik Dahiru Usman Bauchi, inda aka gudanar da addu’oi, Lakcoci, ƙasidu da sauran abubuwan da suke da alaƙa da Maulidin.

Al'ummar Jihar Bauchi Sun Gudanar Da Gagarumin Maulidi

Da yake jawabi Sheik Dahiru Usman Bauchi ya yabawa Gwamnan Bala Muhammad, dama al’ummar jihar a bisa goyon bayan da suka bayar, harma ya ƙaddamar da Littafin dake ƙunshe da tarihi da kuma darussan rayuwar sa.

A nasa ɓangaren Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad, ya yabawa waɗanda suka shirya Maulidin duba da yadda ya ɗabbaƙa zaman lafiya da ƙaunar juna.

Al'ummar Jihar Bauchi Sun Gudanar Da Gagarumin Maulidi

Gwamnan wanda ya sami wakilcin Mataimakinsa, Jatau, ya ce duk da wani muhimmin aiki yasa ya tafi jihar Edo amma zuciyarss tana nan, saboda muhimmancin da Maulidin yake da shi.

Harma Mataimakin Gwamnan ya bawa masu shirya taron Maulidin kyautar naira Milyan Goma a madadin Gwamnan.

 

Al'ummar Jihar Bauchi Sun Gudanar Da Gagarumin Maulidi

Sanarwar da Mashawacin Gwamnan Bauchi a Kafafen Sada Zumunta, Alhaji Nuru Abdullahi (Baban Zarah) ya aiko wa jaridar GTR Hausa ta ce, ɓangarori da dama sun bayyana Maulidin a matsayin wanda aka sami gagarumar nasara, duba da yadda ya kasance mafi ƙayatarwa a baya-bayan nan.

Taron Maulidin ya sami halartar manyan baƙi irin su Gwamnoni, Sanatoci, Sarakunan Gargajiya da dai sauransu.

About gtrhausa

Check Also

Jam'iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

Jam’iyyar NNPP Ta Canza Ɗan Takarar Kujerar Shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotso

               Daga Bello Usman.   Jam’iyyar NNPP ta sauya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar