Home / Flooding / Ambaliya : Zauren Haɗin Kan Malaman Kano Ya Ƙudiri Aniyar Tattara Kayan Tallafi, Domin Kaiwa Yankin Arewa Maso Gabas

Ambaliya : Zauren Haɗin Kan Malaman Kano Ya Ƙudiri Aniyar Tattara Kayan Tallafi, Domin Kaiwa Yankin Arewa Maso Gabas

Ambaliya : Zauren Haɗin Kan Malaman Kano Ya Ƙudiri Aniyar Tattara Kayan Tallafi Domin Kaiwa Arewa Maso Gabas              Daga Bashir Gasau.

 

Zauren haɗin Malaman Kano da ƙungiyoyin Musulunchi na jihar Kano, ya samar da kwamitin tattara kayan tallafi, domin kaiwa mutanen da Iftila’in ambaliyar ruwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya shafa.

Sakataren Zauren Dakta Saidu Ahmad Dukawa ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Jihohin da suka ƙudiri aniyar kai tallafin sun haɗar da Maidugurin Jihar Borno, Yobe da kuma Adamawa.

Dakta Dukawa ya ƙara da cewa, gudunmawar da ake buƙata ta haɗar da ta kuɗi, abinci, suttura, kayan yara, kayan amfanin mata da dukkan wani nau’i na buƙatun yau da kullum.

Sanarwar ta kuma bayyana lamarin a matsayin babbar Jarrabawa, wadda take buƙatar addu’a da kuma tallafi daga wurin al’umma.

Adan haka ne Zauren yayi kira ga kafatanin al’umma da su dage wajen taya waɗanda ibtila’in ya ritsa da su, da addu’ar neman sauƙi daga wurin Allah Maɗaukakin Sarki.

Ga dukkan masu buƙatar bada tasu gudunmawar zasu iya kaiwa Masallacin Juma’a mafi kusa da su, idan kuma Kuɗi ne za’a iya saka wa a asusun Kungiyar kamar haka:

Banki : Jaiz bank

Lambar Asusu : 00 03 60 65 73

Sunan Asusun : NUSAID HUMANITARIAN INITIATIVE

A ƙarshe Zauren yayi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, ya warkar da waɗanda suka jikkata, ya mayar da arzikin da aka rasa, ya kuma kiyaye afkuwar makamancin wannan ibtila’in anan gaba.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar