Daga Bashir Gasau.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a ƙara tallafawa mutanen da Iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maidugurin Jihar Borno.
Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Malick ne ya buƙaci hakan a yayin da ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa jihar Borno, domin jajantawa waɗanda Iftila’in ya shafa.
Tawagar ta gana da waɗanda Iftila’in ya shafa harma suka jaddada aniyar su na tallafawa yunƙurin Gwamnati, da tallafa musu ta hanyar fito da hanyoyin da za’a magance musu matsalolin da suke ciki.
Sanarwar da Shugaban sashen yaɗa labaran Majalisar a Najeriya Ann Weru ya aiko wa jaridar GTR Hausa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, kimanin Mutane 300,000 cibiyar bada agajin gaggawa ta jihar ta canza wa matsuguni a ƙwaryar birnin Maiduguri da ƙananan Hukumomin Jere da kuma Konduga.
A yayin ziyarar, tawagar ta ziyarci Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum domin jajanta musu a bisa Iftila’in ambaliyar, wadda ta haddasa asarar Rayuka dama dukiya me ɗumbin yawa.
Daga cikin matsugunin wucin gadi sama da 25 da aka tsugunar da mutanen, tawagar ta ziyarci Furamaren Asheik Jarma da kuma Sakandiren ‘Yanmata ta Yerwa.
Harma suka ganewa Idon su irin halin da al’ummar suke ciki a sakamakon yadda ambaliyar ta raba su da muhallansu, kasuwancin su dama dukkan wasu abubuwan buƙatar rayuwar yau da kullum.
Adan haka Majalisar ta ayyana shirin ta na kashe Dala Milyan 8 domin samawa al’ummar matsuguni na din-din-din, domin tabbatar da cewa basu haura mako biyu a wuraren wucin gadin da suke ba.
Haka kuma za’a yi amfani da ƙarin tallafin da aka samu, wajen sama musu sauran kayan da suke buƙata domin ya zama sun tsaya da ƙafafun su.
Da yake jawabi Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yaba wa Majalisar Ɗinkin Duniya dama sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu.
A bisa gudunmawar da suka bawa jihar dama waɗanda lamarin ya shafa, ta hanyar amfani da jirgin su domin ceton al’umma, basu kayan abinci dama na sauran buƙata.
Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ƙunshi Shugabannin Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Daraktoci daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, Ƙungiyar Red Cross da dai sauransu.
Haka kuma kwamitin ya ce Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, ta bashi rahoton yadda ambaliyar ruwa ta shafi sama da Mutane Milyan guda a Jihohi 7 dake sassan Najeriya.