Daga Bello Usman.
A yau Lahadi ne Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida Najeriya, bayan kammala ziyarar aiki a ƙasar China da kuma birnin London.
Mashawacin Shugaban ƙasar a fannin yaɗa labarai Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.
Inda ya ce a ranar 29 ga watan Agusta ne Shugaba Tinubu ya bar Najeriya zuwa Beijing na ƙasar China, inda ya yada zango a Dubai kafin daga bisani ya isa ƙasar a ranar 1 ga watan Satumbar nan da muke ciki.
Kuma a yayin ziyarar aikin nasa wanda ya fara a ranar biyu ga Satumbar, sun tattauna da Shugaban ƙasar China Xi Jinpin, harma ƙasashen biyu suka sanya hannu akan yarjejeniya da ya ƙunshi ayyuka 5 a lokacin tattaunawar.
Haka kuma Tinubu ya ziyarci Kamfanin Huawei da kuma na gina layin dogo mallakar ƙasar, wato China Railway Construction Corporation (CRCC).
Kafin daga bisani a yammacin ranar Shugaban ƙasar China da Matarsa Peng Liyuan suka shirya wa Shugaba Tinubu wasan al’adun su na ƙasar China.
Bayan Tinubu ya bar Birnin Beijing na ƙasar China, ya wuce Birnin London inda ya shafe kwanaki a can.
Harma a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya gana da Sarki Charles, inda suka tattauna akan batutuwan da suke da alaƙa da sauyi yanayi.