Daga Aliyu Gerengi, Gombe.
Gidauniyar dake tallafawa Marayu da marasa ƙarfi ta jihar Borno wato Bilal Charity Care Foundation (BCCF), ta tallafawa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a birnin Maiduguri.
Shugaban Gidauniyar na jihar Kwamared Bilal Muhammad Ali Biu ne ya bayyana hakan, a yayin da tawagar ƙungiyar ta ziyarci ɗaya daga cikin wuraren da aka tsugunar da mutanen domin miƙa musu tallafin.
Kuma dai kayan da Gidauniyar ta kai sun haɗar da maganin Sauro da kuma Tufafi na Mata da Maza.
Da yake yiwa jaridar GTR Hausa ƙarin haske, Shugaban Gidauniyar ya ce sun ɗauki matakin tallafa musu ne domin rage musu raɗaɗin Jarrabawar da ta same su.
Harma ya buƙaci al’ummar da suke son tallafawa da dukkan wani abin buƙata, zasu iya kaiwa Ofishin Gidauniyar dake Bolori 2 Umarari, daura da Furamaren B-Charity a Maidugurin jihar ta Borno.
Haka kuma ga masu son tura Kuɗi domin a siya musu abubuwan buƙata, zasu iya turawa ta Asusun Gidauniyar kamar haka;
lambar Asusu : 5441835347
Sunan Asusu : Bilal Charity Care Found.
Sunan Banki : Moniepoint MFB.
Ga dukkan masu neman ƙarin bayani zasu iya kiran lambobin gidauniyar wato 07066943328 ko 08061327567 , domin neman ƙarin bayani akan sauran shirye-shiryen da ake yi akan lamarin.
A ƙarshe sunyi fatan Allah ya bada ikon taimakawa kuma ya kare faruwar hakan a nan gaba.