Daga Bashir Gasau.
Gwamnatin Jihar Kano ta bada tallafin Naira Milyan ɗari, ga waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maidugurin Jihar Borno.
Tawagar Gwamnatin Kanon ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan yaɗa Labarai, Baba Halilu Dantiye ne suka miƙa takardar Cakin Kuɗin ga Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a yayin ziyarar jajen da suka kai jihar.
A saƙon Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ga waɗanda iftila’in ya shafa, ya bayyana lamarin a matsayin wata Jarrabawa da suke buƙatar cikakkiyar gudunmawar daga kowanne ɓangare.
Adan haka Gwamnatin ta bada nata tallafin domin nuna sadaukarwa ga jihar Borno a wannan lokaci na tsanani da take ciki, harma ta yi fatan Allah ya kare faruwar hakan a nan gaba.
A nasa jawabin Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano dama al’ummar jihar a bisa irin gagarumar gudunmawar da suka bayar, inda ya bada tabbacin bada tallafin ga waɗanda iftila’in ya rutsa dasu.
Zulum ya kuma bayyana irin wannan aikin tausayi a lokacin yanayi na tsanani, a matsayin abinda zai ƙara haɗa kan Jihohin Najeriya.
Wannan tallafi dai ya ƙara nuna irin daɗaɗɗiyar alaƙar ‘yan uwantaka dake tsakanin Jihohin biyu.
A ƙarshe Gwamnan Kano yayi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar, ya kuma bawa waɗanda suka jikkata lafiya.
Tawagar Gwamnatin Kano ta ƙunshi Kwamishiniyar kula da harkokin Jin-ƙai dama yaƙi da talauci, Hajiya Amina Sani, Mashawacin Gwamnan akan tsare-tsare da ci-gaban al’umma Dakta Danyaro Yakasai da dai sauransu.