Home / Business / Farashin Litar Man Fetur Ya Koma Naira 999 A Kano Da Kaduna – NNPCL

Farashin Litar Man Fetur Ya Koma Naira 999 A Kano Da Kaduna – NNPCL

Farashin Man Fetur Ya Koma Naira 999 A Kano Da Kaduna - NNPCL.           Daga Bello Usman.

 

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ce farashin Man Fetur ya koma Naira 999.22 a Jihohin Kano da Kaduna.

NNPCL ya sanar da hakan ne ta cikin sanarwar jadawalin farashin man da ya fitar, bayan siyo shi daga matatar man Ɗangote.

Farashin Man Fetur Ya Koma Naira 999 A Kano Da Kaduna - NNPCL.

Kuma dai ga jerin farashin Man a gidajen mai na NNPC a faɗin ƙasar, inda jihar Legas ce zata fi samun sassauci.

Legas – N950.22

Oyo – N960.22

Rivers – N980.22

Sokoto – N999.22

Kano – N999.22

Kaduna – N999.22

FCT – N999.22

Borno – N1,019.22

A sanarwar NNPCL ta safiyar yau Litinin, ta ƙara da cewa bisa tsarin dokar albarkatun man fetir ta ƙasa, gwamnati ba ta da hurumin fayyace farashin mai, sai dai ana fitar da farashin ne bayan tattaunawa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a harkar.

Sanarwar ta kara da cewa saɓanin yadda yake a rahotanni, kamfanin zai rinƙa sayen man daga Ɗangote da dalar Amurka har ƙarshen watan Satumba, inda sai ranar 1 ga watan Oktoba ne kamfanin zai fara biyan Ɗangote da naira.

Kamfanin ya ƙara da cewa “idan ƴan Najeriya ba su gamsu da farashin ba, to da zarar kamfanin Ɗangote ya yi ragi to su ma za su gaggauta yi wa ƴan Najeriya ragin ɗari bisa ɗari.” In ji sanarwar.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar