Daga Aliyu Gerengi, Gombe.
Gamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Muhammad, ta yi Allah-Wadai da kalaman Sanatan Bauchi ta kudu Senator Shehu Buba.
Na zargin Ma’aikatan hukumar Sintirin jihar da hannu wajen kisan da ya faru a ƙauyen Zaranda dake ƙaramar hukumar Toro.
Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida na jihar Abubakar Abdulhamid Bununu ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa.
Da Mashawacin Gwamnan Bauchi kan kafafen sada zumunta Alhaji Nuru Abdullahi (Baban Zarah) ya aiko wa jaridar GTR HAUSA.
A inda Kwamishinan ya bayyana waɗancan kalamai a matsayin marasa tushe dama yunƙurin kawo rarrabuwar kai domin ɓata sunan Gwamnati dama Hukumomin tsaron jihar.
Baya ga haka sanarwar ta bayyana kalaman Sanatan a matsayin yunƙurin siyasantar da lamuran tsaron jihar, ba tare da duba illar da hakan zai haifar ba.
A cewar Abubakar Bununu “Kalaman Sanata na zargin yin sakaci abu ne da Gwamnatin da Hukumomin tsaron jihar ba zasu amince da shi ba, duba da yadda ya kasance salo na ƙoƙarin sare gwuiwar Hukumomin tsaro dama kawo tunzuri a tsakanin al’ummar jihar”.
Haka kuma Gwamnatin ta bada tabbacin gudanar da cikakken bincike akan kisan na Zaranda, ta hanyar gano waɗanda suke da hannu kuma a hukunta su, domin ganin anyi wa kowanne ɓangare adalci akan lamarin.
Adan haka ne sanarwar ta buƙaci Sanatan ya janye kalamansa kuma ya nemi afuwar al’ummar jihar, a bisa wannan kalaman nasa da marasa kyau.
Bugu da ƙari Gwamnatin ta yi kira ga Hukumomin tsaro da su gayyaci Sanatan domin ya bada bahasi akan kalaman nasa.
Tuni ita mah Jam’iyyar APC ta jihar tayi Allah-Wadai da kalaman Sanatan, inda ta bayyana shi a matsayin abin takaici da baƙin ciki.
A ƙarshe suma al’ummar jihar sun bayyana takaicin su da kalaman, inda suka ja hankalin sa da ya maida hankali wajen magance matsalar dake damun waɗanda yake wakilta, maimakon yaɗa Labaran da basu da tushe.