Daga Bello Usman.
Wani Ɗan jarida mai zaman kansa a jihar Kano, Idris Usman Rijiyar Lemo, ya shawarci gwamnatin jihar da ta samar da hukumar kula da makarantun Islamiyyu da Tsangayu.
Ɗan jaridar ya bada shawarar ne a yayin zantawar sa da jaridar GTR Hausa, inda ya ce ta hakan ne za’a bunƙasa ilimin Al’qur’ani da litattafai, baya ga kyautata rayuwar Malamai ta hanyar basu duk wata kulawar da suke da buƙata.
A cewar sa “Yin kiran ya zama wajibi la’akari da yadda ake samun taɓarɓarewar tarbiyya a tsakanin yara da matasa, a wani lokacin ma har da magidanta da matan aure a sakamakon rashin kulawar da ɓangaren Ilimin Addinin yake samu”.
Haka kuma ya bayyana ci-gaba da samun faruwar hakan a matsayin babbar barazana ga rayuwar al’ummar dake tasowa, duba da yadda matuƙar ba’a ɗauki matakin gaggawa ba lamarin bazai haifar da Ɗa mai ido ba.
Bugu da ƙari ya danganta rashin samun kulawa daga wurin iyayen dalibai da attajiran unguwa, a matsayin abinda ke ƙara ta’azara matsalar duba da yadda ake fifita karatun boko akan na Addini.
Adan haka ya ce akwai buƙatar gwamnatin Kano ta tsaya tayi duba na tsanaki, akan halin da Makarantun Islamiyyu dana Tsangayu suke ciki, ta hanyar samar musu da hukumar da zata dinga basu kulawar da ta kamata.
A karshe Dan Jaridar yayi fatan gwamnati za ta gaggauta yin aiki da shawarar da ya bayar, domin ci-gaban Kano da Al’ummar ta, duba da yadda ake hasashen tafi kowace jiha yawan Mahaddata Al’qur’ani a duk faɗin Duniya.