Home / Flooding / Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa

Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa

Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa      Daga Bashir Gasau.

 

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada tallafin Naira Milyan 250, ga waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maidugurin Jihar Borno.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ne ya tabbatar da hakan, a yayin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar domin zuwa ziyarar jaje, ga Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum dama al’ummar jihar musamman waɗanda Iftila’in ya shafa.

Sanarwar da Mashawacin Gwamnan akan kafafen sada zumunta, Alhaji Nuru Abdullahi (Baban Zahra) ya aiko wa jaridar GTR Hausa ta ƙara da cewa, Gwamnatin ta kuma ƙara da bada tallafin kayan amfanin yau kullum kamar Abinci, Tufafi da kuma kayan aikin gini.

Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa

A cewar Gwamnan Bauchi “Akan batun fannin lafiya kuma mun shirya bada cikakkiyar gudunmawa, domin magance ƙalubalen da za’a iya fuskanta a fannin domin ganin waɗanda suka jikkata sun sami sauƙi cikin gaggawa”.

A nasa ɓangaren Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana matuƙar godiyarsu da wannan tallafi na nuna sadaukarwa, harma ya ce tallafin ya ƙara musu ƙwarin gwuiwar samawa al’ummar su sauƙi a halin da suke ciki.

Ambaliyar Maiduguri : Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Bada Tallafin Naira Milyan 250 Ga Waɗanda Iftila’in Ya Shafa

Haka kuma Zulum ya bayyana ziyarar a matsayin wadda zata ƙara ƙulla zumunci a tsakanin Jihohin biyu, harma ya bayyana irin wannan aikin tausayi a lokacin yanayi na tsanani, a matsayin abinda zai ƙara haɗin kan juna.

A ƙarshe Gwamnan Bauchi yayi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a sakamakon ambaliyar, ya bawa waɗanda suka jikkata lafiya, kuma ya maida dukkan asarar da aka yi.

About gtrhausa

Check Also

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

Gwamnatin Najeriya Ta Bude Shafin Bawa Matasa Adaidaita Sahu Me Amfani CNG

         Daga Auwal Durumin Iya. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta buɗe shafin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Skip to toolbar