Daga Bashir Gasau.
Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya miƙa saƙon jaje ga al’ummar Maidugurin Jihar Borno, a bisa Iftila’in ambaliyar ruwan da ya same su.
Sarkin ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran sa, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya aiko wa jaridar GTR Hausa, inda ya bayyana ibtila’in a matsayin wani babban abin da ya girgiza al’ummar Ƙasar nan baki-ɗaya.
A cewar Sarkin Kano na 15 “Ba kasafai aka fiye samun irin wannan mummunar ambaliya ba, amma idan hakan ta faru to babu abunda ya kamata al’umma su yi, sai addu’ar Allah kada ya sake maimaita wa.
Daga nan sai ya sake miƙa jajensa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Alhaji Kashim Shettima, dama Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum harma da Shehun Borno Alhaji Mustapha El Garbai.
A ƙarshe Sarkin yayi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu ya kuma bada lafiya ga waɗanda suka jikkata, tare da mayar da mafificin alheri ga waɗanda suka rasa dukiyoyinsu.