Daga Bashir Gasau.
Fadar Sarkin Gumel dake jihar Jigawa ta sanar da ranakun bikin Sallar Gani na wannan shekara.
Fadar ta sanar da ranar Sallar Ganin ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar, Alhaji Murtala Aliyu (Maji-Dadin Gumel) ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar Sanarwar “Mai Martaba Sarki yana sanar da Masu Girma ‘Yan Majalisa Sarki, Hakiman Gundumomi, da kuma Hakiman Karaga cewa ya Majalisar Masarautar ta amince da ranakun gudanar da bukukuwan Gani ta wannanshekara 2024/1446 AH”.
Kuma dai ranaku Ukun da Masarautar ta sanya sune;
(1) Juma’a 20/9/2024.
(2) Asabar 21/9/2024.
(3) Lahadi22/9/2024
Adan haka sanarwar ta ce ana umartar dukkan ‘Yan Majalisar, Hakimai masu Gundumomi dama Hakiman Karaga su kasance cikin shiri.
A ƙarshe Masarautar ta yi fatan Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairi, ya kaimu lokacin, kuma ya bamu lafiya da zaman lafiya, Ameen.