Daga Bashir Gasau.
Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dakta Dauda Lawal, ta bada tallafin Naira Milyan 20 ga iyalan waɗanda Iftila’in kifewar Kwale-Kwale ta ritsa da su a ƙaramar hukumar Gummi.
Muƙaddashin Gwamnan jihar Zamfara Mani Mal Mummuni Masamar Mudi ne ya miƙa tallafin, a yayin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar zuwa ziyarar jaje da ta’aziyyar waɗanda suka rasu a sakamakon kifewar Kwale-Kwalen.
Sanarwar da Daraktan yaɗa labaran Muƙaddashin Gwamnan, Mikailu Muhammad ya aiko wa jaridar GTR HAUSA ta ce, an damƙa tallafin ne a hannun Shugaban kwamitin yankin Alhaji Salihu Mai buhu Gummi.
the
Da yake jawabi Muƙaddashin Gwamnan ya ce, ya karɓi ƙorafin Kantoman ƙaramar hukumar dama al’ummar jihar kan buƙatar samar musu sabbin Jiragen ruwa na zamani, harma ya bada tabbacin isar da koken nasu zuwa ga zaɓaɓɓen Gwamnan jihar.
Ya kuma miƙa saƙon jaje ga ‘yan Uwa da iyalen waɗanda suka rasa rayukansu, inda yayi fatan Allah ya karɓi shahadar su.
Daga ƙarshe yayi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar dama na Jihar Zamfara gaba-ɗaya, da su ƙara dagewa da Addu’ar Allah ya ƙara bawa Gwamnatin jihar nasara akan ‘yan ta’adda.