Daga Rabi’u Usman.
Guda daga cikin masu buƙata ta musamman a jihar kano, Aminu mai Doki Sharada, yayi kira ga gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusif, da ya cika alƙawarin da yayi musu na samar musu da Ma’aikatar kula da masu buƙata ta musamman.
Mai Doki Sharada dai na wannan kira ne a zantawar sa da jaridar GTR Hausa, inda ya ce sun ji shiru ne akan alƙawarin da Gwamnan Kano yayi musu a lokacin yaƙin neman zaɓe.
A cewar Mai Doki “muna fatan Gwamnan Kano zai cika alƙawarin da yayi mana a lokacin da yake neman ƙuri’armu, wanda hakan ce ta sanya muka zuba masa ruwan ƙuri’u amma kuma yanzu yana neman mantawa damu”.
Haka kuma yace masu buƙata ta musamman suna cikin wani mawuyacin hali, musamman a irin wannan lokaci na durƙushewar tattalin arziki a jihar kano dama ƙasa baki-ɗaya.
Adan haka ne ya ce suna fatan Gwamnan Kano zai taimaka ya cika wancan alƙawari da ya yi, duba da yadda a lokacin baya ya shaida musu cewa shirye-shirye samar da Ma’aikatar yayi nisa.
A ƙarshe yayi fatan Gwamnan Kano zai ji wannan kira da yayi ta hanyar amsa tunin da yayi masa domin samar da Ma’aikatar, wadda ya ce za ta taka muhimmiyar rawa ga rayuwar dukkan wani me buƙata ta musamman dake faɗin jihar.